By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani rukunin gidaje masu karamin karfi na Kofar Gayan da ke Zariya a jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da wani jami’in kwastam, Muawiyya Gambo Turaki, da dansa Khalifa da wasu mutane takwas.
DUBA WANNAN LABARIN: Sauya Sheka: Majalisar Dokokin Jihar Kwara Ta Bayyana Kujerar Wani Dan Majalisar A Matsayin Wacce Babu Kowa
Har yanzu dai kakakin rundunar ‘yan sandan Muhammad Jalige bai samu cikakken bayani kan lamarin ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, sai dai mazauna yankin sun shaidawa jaridar The Nation cewa ‘yan bindigar sun mamaye yankin ne da misalin karfe 9:00 na daren Laraba.
Wannan dai shi ne karo na biyu da ake kai wa Kofar Gayan hari cikin watanni shida da suka gabata. A harin na farko, an yi garkuwa da matar wani jami’in kwastam da wata mata, daga baya kuma an sako su bayan an biya kudin fansa naira miliyan 15.
Wani mazaunin unguwar, Yishau Aisha, ya ce, “wadanda suka yi garkuwa da su takwas ne kuma sun zo da kafa da manyan makamai. Sun yi ta faman yi mana magana da harshen Hausa; harshensu na fulani ne.
“Ina ganin masu ba da labari ne ke haddasa wadannan sace-sacen mutane ba tare da katsewa ba, domin da alama babban burinsu shi ne jami’in kwastam da ya dawo gida daga bakin aikinsa kwana guda sai a sace shi.”
Haka kuma wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani David Onoja, shugaban gidauniyar Enemona Josh Humanitarian Foundation a gidansa dake hanyar Wada, Lokoja, jihar Kogi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, William Ovye-Aya, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN faruwar lamarin a jiya.
Ovye-Aya, ya nakalto majiyar iyalansa, ta ce wasu ‘yan fashin daji shida sanye da kakin ‘yan sanda sun dauke Onoja daga gida da misalin karfe 10:30 na safiyar jiya.