Wasu matasa da ake kyautata zaton yan daba ne da aka yi hayar su sun farmaki tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Bayelsa Boyelayfa Debekeme.
Kazalika matasan sun farmaki tawagar hadimin gwamnan jihar kan ayyuka da kere-kere Famous Daunimughan.
Ana kuma kyautata zaton wannan farmaki ba zai rasa nasaba da yunkurin mutanen na halartar taron samar da yan takara a kujerar Sanatan Bayelsa ta yamma ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an hayo matasan ne da zummar tarwatsa taron gami da sanya fargaba a zukatan mahalarta taron da suka kasnace ƴaƴan PDP.
Sai dai hakan kamar yadda rahotannin suk bayyana bai dakatr da taron ba, amma shugabanni da dattawan yankin sun yi Allah wadai da hakan.