‘Yan sanda sun kama mutum 17 da ake zarginsu da laifukan fashi da makami da kuma ƙungiyar asiri a sassa daban-daban na jihar Benuwe.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mukaddas Garba ya gabatar da su a garin Makurdi, inda ya ce daga cikinsu akwai ‘yan asalin jihar Nasarawa da Filato dsa suka yaudari wani dan acaba zuwa wani otal suka ba shi maganin barci suka gudu da babur ɗinsa.
An kuma kama wasu ‘yan fashi da suka shiga wani gida a unguwar GRA ta garin Makurdi, suka ƙwace wayayoyin hannu ƙirar Iphone 11 Promax da infinix; da jakar agoguna; sa’annan suka yi amfani da wayar suka tura miliyan ɗaya cikin asusun wani da suka buɗe don karkatar da kuɗin.
Ya ƙara da cewa, a lokacin binciken an samu waɗanda ake zargin da ke zaune a wurare daban-daban da kayan.
https://dimokuradiyya.com.ng/mutane-9-sun-rasa-rayukansu-yayin-da-yan-fashi-suka-shiga-banki/
Daga cikin abubuwan da aka samu hannunsu, kamar yadda ya gabatar, akwai kuɗi N300,000 da wayar hannu ƙirar Iphone 11 Promax da kuma jakar agogunan da aka sace wa wani mutum.
Daga cikin mutanen da aka gabatar akwai wani da ke unguwar Wadata, Makurdi da aka kama bisa zargin fashi da makami.
Kwamishinan ya ce an samu talabijin (plasma) da De-Tech recorder da igiyar yawo ta lantarki da sauran kayayyakin da aka sace a inda aka yi fashin.
Kwamishinan ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin fashi da makamin kuma za a kai shi kotu ta yanke masa hukuncin da ya dace da shi.