Fadar shugaban kasa ta fusata da irin rubuce-rubucen sukar gwamnati da ake yi a wadansu jaridun kasarnan inda suka nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi ne ke mulkin kasarnan ba.
Fadar shugaban kasar ta bayyana hakan ne a sanarwar da Kakakin shugaban Nijeriya, Malam Garba Shehu ya fitar aka raba a Abuja a ranar Lahadi.
A cewarsa mutane da daman na rubuce-rubuce a jaridu da sunan sharhi, amma a cewarsa masu rubuce-rubucen kawai suna magana ne da harshen ‘yan adawa. “Mutanen da suka lalata kasarnan cikin shekara 16 na mulkin rashawar da suka yi.”