Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wato Femi Adesina ya ce ya zama lallai ya fargar da ‘ƴan Nijeriya kan wata manaƙisa da wasu kafofin yaɗa labarai na intanet ke shiryawa don ɓata wa Shugaba Muhammadu Buhari suna.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Adesina ya ce a kwanan nan ne shafukan za su fara fitar da labarai da rahotanni da suka shirya musamman don rura wutar rikici a ƙasar. Ya ce suna da niyyar nuna Shugaban a matsayin mai nuna son kai da nuna ɓangaranci. Wannan ya saɓa wa alƙawarin da ya yi wa ‘ƴan Nijeriya na zama na kowa.
Adesina ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa masu son tada zaune tsayen sun saye shafukan inatnet da jaridun da ke shirin fitar da rahotannin da ke zargin shuga Buhari da nuna wariya ga wani addini ko ɓangare.