Wasu karin yan majalisar dokokin jihar Kano guda uku sun sauya sheka zuwa jamiyyar NNPP mai lakabin kayan marmari.
Sanarwar da daraktan yada labarai na Majalisar Uba Abdullahi, ya fitar a Larabar nan ta bayyana cewa shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya karbi wasikar sauya shekar da ‘yan majalisun suka mikawa zauren.
‘Yan majalisun da sukai canjin shekar sun hada da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, Abdullahi Iliyasu Yaryasa, da Muhammad Bello Butu-butu, mai wakiltar karamar hukumar Rimin Gado da Tofa, sai kuma Honorable Kabiru Yusuf Ismail mai wakiltar Karamar hukumar Madobi.
A yan kwanakin nan dai yan siyasar da aka batawa daga jam’iyyu daban-daban na komawa jamiyyar ta NNPP domin samun mafaka.
Yanzu haka dai Tsohon Gwamnan Kano shine jagoran jam’iyyar, wanda kuma wasu ke ganin yana da alaka wajen komawar mutanen sakamakon yadda da tarin magoya baya.