Tsohon kakakin rundunar soji, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka mai ritaya ya caccaki wasu yan Nigeria, wadanda ya ce, ba sa jindadin kokarin da jami’an tsaro ke yi, wajen ci gaba da kai farmaki kan yan fashi da sauran masu aikata laifuka a Arewa maso Yammacin kasar nan.
Kukasheka ya bayyana hakanne a yau Litinin, ta shafinsa na Facebook.
Inda ya wallafa cewa, “Ga dukkan alamu, wasu mutane ba sa farin ciki da kwazon jami’an tsaron mu, dake aiki a yankin Arewa maso Yamma”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mahara sun hallaka Malamin Cocin ECWA a Kaduna
“Amma Muna matukar farin ciki da jami’an tsaro, kuma muna rokon su da su ci gaba da kai farmaki kan yan bindiga.”
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta lura cewa, a cikin yan kwanakin da suka gabata, jami’an tsaron Nigeria, sun tsananta kai hare-hare kan Yan bindiga da masu Garkuwa da mutane, da sauran masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
Kazalika Rahotannin da ke fito wa daga Arewa maso Yamma na nuna cewa, yan bindiga ba sa samun sauki, saboda aikin soji dake gudana a shiyyar, saboda an kashe da yawa daga cikinsu, yayin da ake kuma kama wadanda ke kokarin tsere wa.
Comments 2