By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasa biyu ne aka ruwaito sun nutse a cikin dam din dake Rayfield Resort Jos ta jihar Plateau.
Wadanda lamarin ya rutsa dasu dai sun hada da Michael Nyam mai shekaru takwas da kuma Elijah Solomon dan shekaru shida.
Wani ganau mai suna Mista Gyang Pwol, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya ranar Lahadi a Jos cewa yaran sun nutse ne da yammacin ranar Asabar.
Ya ce dukkansu mazauna unguwar Rayfield ne.
Pwol ya bayyana cewa mutanen biyu sun nutse ne a lokacin da suke kokarin dawo da takalmin daya daga cikin abokansu da ya fada cikin dam din.
“Sun yi tsalle cikin zurfin ruwa a cikin dam don ceto wani takalmin abokinsu, abin takaici, yawan ruwan ya yi yawa.
“Kafin a kawo musu taimako duk, sun nutse,” in ji shi.
Pwol, wanda kuma ya tabbatar da cewa an binne gawarwakinsu, bai yi karin bayani ba.
Sai dai ASP Ubah Ogaba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, ya ce ba a kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda ba.
(NAN)