Wata ƙungiya ta Jam’iyyar PDP tayi kira ga Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike daya fito takarar Shugaban Ƙasa a shekarar 2023.
Sunyi wannan kiran ne a Calabar, Babban Birnin Jahar, inda suka bayyana cewa Gwamna Wike nada sani a fannin tattalin arziki da Siyasa dazai ciyar da Ƙasar nan a gaba.
Sun ƙara dacewa ƙasar nada buƙatar shugaba irin Wike.

KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Kwallon Kafa Ta Faransa Ta Tabbatar Da Raunin Pogba
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar kammala taro da Jigon Jam’iyyar PDP Gab Odu Oji a Jahar Cross River ya fitar, yana mai cewa Wike nada abubuwan da ake buƙata domin ceto ƙasar nan.
“Wike ɗan ƙasa ne nagari, wanda yayi imani akan haɗin kan Najeriya, kuma ya nuna hakan a lokacin Gobara a Sokoto.”
“Wike mai ceto ne, muna ganin zai iya ceto ƙasar nan”, inji sanarwar.