Wata Ƴar Ƙaramar Yarinya Data Shafe Watanni 3, Ta Mutu Bayan Kwanaki 5 Da Sakin Ta
Wata ƙaramar yarinya mai suna Ewhalshoh Mandela Mairabo, wadda aka yi garkuwa da ita tare da mahaifiyarta da wasu 29, ta rasu kwanaki biyar bayan an sako ta.
Wasu ƴan bindiga sun kai hari Dogon-noma a unguwar Maro, Ƙaramar Hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, a watan Mayun 2022, inda suka yi garkuwa da wadda ta mutu, mahaifiyarta, da wasu mutane 29.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyyar PDP za ta Ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman Zaɓen Shugaban Ƙasa
Sai dai kuma bayan tattaunawa da ƴan bindiga, an tilastawa iyalan wadanda abin ya shafa biyan Naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa kafin su samu ƴancinsu.
Wata Majiya mai tushe ta shaida wa DAILY POST a Kaduna a ranar Alhamis cewa, sun biya kudin fansa, yayin da aka sako ƴar uwarsu da Ƙaramar yarinyar a ranar 30 ga Agusta, 2022, bayan sun kashe daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
Amma bayan kwanaki biyar da sakinsu, ta mutu.
DSP Mohammed Jalige bai amsa kiransa na tabbatarwa ba.
A wani labarin kuma: Jam’iyyar PDP za ta Ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman Zaɓen Shugaban Ƙasa
Donald Trump ya sake wani jawabi kan yaƙin neman zaɓe na shiga fadar White House a shekarar 2024, inda tsohon shugaban na Amurka ya shaidawa gidan talabijin na Indiya cewa, tsayawa takara zai farantawa mutane da yawa farin ciki.
“Kowa yana so in tsaya takara. Ni ne ke kan gaba a zaben,” in ji Trump a wani bangare na wata hira da NDTV tayi dashi a ranar Alhamis.