Wata babbar ƙaddara data afkawa Timo Werner tun bayan zuwansa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea dake ƙasar Ingila abin da ake ganin kamar bashi da nasara a zuwansa ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Chelsea a dukkanin wasannin da yake bugawa Chelsea.
Shidai Timo Werner ya kasance tun bayan zuwansa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea idan zai bugamata wasa kokuma zai bugawa Germany wasa to indai zai jefa ƙwallo a wasan to kunnen doki ake tashi ba ayin nasara.
Werner dai Chelsea ta sayo shine domin ya share mata hawayenta na lashe kofuna amma kuma daga fara fafata gasar ajin Firimiya ta Ingila ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Chelsea tana ta fama da rasa maki a kusan kowanne wasa data fafata tun daga farkon kakar wasannan ta bana.
Ga jerin wasannin da Timo Werner ya fafata wanda inda ya jefa ƙwallo to ba’a yin nasara a Chelsea da Germany:
1. Ya buga wasaà daya jefawa Brighton ƙwallo inda a wasan an tashi 1-1 tsakanin Brighton da chelsea.
2. Ya jefa ƙwallo a wasan da aka tashi 1 da 1 tsakanin Germany da spain.
3. Chelsea da Tottenham sun buga wasa sun tashi 1 da 1 kuma Timo Werner ne ya jefa ƙwallon.
4. A wasan da Germany ta buga 3 da 3 da Switzerland Timo Werner ya jefa ƙwallo amma kunnen doki aka tashi.
5. Haka zalika a wasan mako na 5 da aka fafata tsakanin Chelsea da Southampton wasan da aka tashi 3 da 3 shima Timo Werner ya jefa ƙwallo.