A wannan rana ta Alhamis wato 24 ga watan Satumba na shekarar 2020 za a fafata wasan ƙarshe na gasar Super Cup tsakani ƙungiyar ƙaallon ƙafa ta Bayern Munich da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla dake ƙasar Andalus, shi dai wannan wasa ana fafata shi tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafan da ta lashe gasar zakarun nahiyar turai da kuma wadda ta lashe gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai wato Europa.
Ita dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich itace wadda ta zamo zakara a gasar zakarun ta turai wato kakar wasan da aka kammala kenan kakar wasa ta 2019 zuwa 2020, sai dai Bayern Munich a kakar wasan da aka kammala ta ajiye wasu manyan tarihi daba kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ce take ajiye irinsa ba a gasar duba da irin bajintar da tayi.
Ga wasu daga cikin irin tarihin data kafa.
1. Itace ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta farko data lashe dukkanin wasanninta na gasar zakarun nahiyar turai na kakar wasan da aka kammala kama tun daga rukuni har zuwa wasan zagaye na 16 da wasan kusa dana kusa dana ƙarshe da wasan kusa dana ƙarshe da kuma wasan ƙarshe.
2. Ta shiga jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suka jefa ƙwallaye sama da guda 40 a kakar wasa guda ɗaya inda ta shiga jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Real Madrid da Liverpool harma da Barcelona.
3. Ta shiga jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suka jera wasanni guda goma kokuma suka buga wasanni guda goma ba tare da ansami nasara a kansu ba.
4. Haka zalika Bayern Munich ta zazzagawa manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ƙwallaye da dama inda ta zabgawa Tottenham ƙwallaye 10 gida da waje, sannan ta tafkawa Chelsea ƙwallaye 7 gida da waje, haka ta zazzagawa Crevena Vezda ƙwallaye 9 gida da wace inda ta yiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ruwan ƙwallaye a wasa ɗaya tilo wato ta juyemata ƙwallaye guda 8 rigis a zare inda hakan yayi sanadiyyar kusan wargajewar ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Barcelona.
Bayern Munich dai ta lashe gasar ta zakarun nahiyar turai sau 6 a tarihi inda kawai ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suka fita lashe gasar sune A.C Milan wadda take da guda 7 sai kuma Real Madrid da take da guda 13.
Ita kuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla wadda itace ta lashe gasar Europa league wato gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai inda daman shi kofin ta mayar dashi kamar na gado tunda duk nahiyar turai babu wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa data kaita lashe gasar.
Haka masana harkar wasanni a duniya sunyi ittifaƙin cewar babu wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa data isa ta ɗagawa Sevilla yatsa ba tare data tanƙwarashi ba a amma fa a gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai, a yanzu haka Sevilla ta lashe gasar sau 6 a tarihi inda babu wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa data taɓa lashe gasar sau 4 inda dukkanin masu bin bayan Sevilla kowacce sau 3 ta lashe.
Sevilla dai a wannan kakar wasan ta bana ta kowaya manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na nahiyar hankali musamman a wannan gasar ta Europa data lashe, inda ta wanke A.S Roma, ta zazzagawa Wolves ta koreta, sannan tayi tafiyar ruwa da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United awasan kusa dana ƙarshe, inda Sevilla dai batayi ƙasa a gwiwa ba wajen ragargaje Inter Milan awasan ƙarshe.
Za a fafata wannan wasa na ƙarshe tsakanin Bayern Munich da Sevilla da misalin ƙarfe 8:00 agogon Najeriya da Niger da Cameroon da kuma Chad wanda yayi dai dai da ƙarfe 7:00 agogon GMT da Ghana.