Iyalai 67,106 da ke cikin matsananciyar buƙata sakamakon annobar Korona a jihar Katsina za su samu kayan tallafin.
Gwamnan Jihar Aminu Masari, yayin ƙaddamar da rabon tallafin da ƙungiyar COCOVID-19 ta bayar domin raba wa mabuƙata a jihar.
Ya ce kowannen daga cikin iyalan da aka riga aka tantace zai samu masara da shinkafa da taliya da gishiri da kuma taliyar ‘yan yara.
Wakilin COCOVID-19, Bello Mohammed ya ce kayan na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar na rage wa talakawa matsin da annobar ta jefa su a ciki.
Gwamnan jihar ya ce za a tsaurara matakan tabbatar gaskiya a rabon kayan ta hanyar amfani da sarakuna da ƙungiyoyin kare haƙƙin dan Adam da sauran masu ruwa da tsaki.
Masari wanda ya ce annobar Korona ta tilasta wa gwamnatinsa taƙaita ayyuka a wasu ɓangarori, ya ƙara da cewa suna iya bakin ƙoƙarinsu domin shawo kan cutar da kuma yin wasu ayyuka.