Ƴan sanda a ranar Juma’a a Kaduna, sun kama wata ƴan shekara 23 mai aikin gida, wadda ake zargin ta sace sarƙar gwala-gwalai da darajar ta yakai Miliyan 10.
Aisha Abdullahi ta bayyana a gaban Chief Majistare a Kaduna akan laifuka guda biyu da suka haɗa da makirci da sata.
Mai aikin wadda take zaune a gida na 3 dake kan hanyar Kaita a Kaduna, ta bayyana cewa bata aikata laifin ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta tabbatar da Garkuwa da Tagwayen Basaraken Gargajiya a Kwara
A cewar lauyan gwamnati Chidi Leo, Aisha Abdullahi ta saci sarƙar daga Hajiya Jamila Ahmed dake Rigasa Kaduna. Leo yace Hajiya Jamila ta kawo ƙarar satar a ofishin ƴan sanda na Gabasawa a ranar 3 ga watan Oktoba.
Mai shigar da ƙarar yace wadda ake ƙarar ta aikata laifuka guda biyu da satar sarƙa. Leo ya ƙara dacewa, an kama ƴar aikin a lokacin da aka ganta a cikin kamara a lokacin da take aikata laifin.
Yace laifin ya saɓa da sashe na 59 da 209 na dokar laifuka ta Kaduna ta shekarar 2017.
Majistare Mr Ibrahim Emmanuel ya bada belin wadda ake ƙara akan kuɗi Naira dubu 500,000 tare da gabatar da mutane biyu da zasu tsaya mata, ɗaya daga ciki sai ya kasance ɗan uwanta ne na jini.
Majistaren ya bada umarnin cewa, sai ya kasance wanda ta gabatar yana aiki.
Ya ɗaga shari’ar ya zuwa ranar 29 ga watan Oktoba domin cigaba da sauraren shari’ar.