Daga Nura Ahmad Hassan
Wata babbar kotun shari’ar musulinci da ke zamanta Tsafe a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara a ranar Talatar nan ta raba auren wani mutum mai suna Musa Tsafe da jikarsa Wasila da suka shafe shekaru 23 da yin aure.
Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Malam Bashir Mahe, ya raba auren ne bayan sauraren karar daga bangaren masu gabatar da kara da kuma lauyoyin masu kara.
Mahe ya ce auren Tsafe da Wasila ya saba wa koyarwar Addinin Musulunci.
Alkalin ya ce auren da ke tsakanin ma’auratan ya saba wa Alkur’ani sura ta 3 aya ta 23, shafi na 79 da shafi na 77 na hukunce-hukunce.
Ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan gazawar lauyan da ke kare wanda ake tuhuma ya tabbatar da hakan.
Hukumar Hisbah ta shigar da kara ne inda take neman a raba auren mai shekaru 23.
Hukumar ta shaida wa kotun cewa auren Tsafe da Wasila ya saba wa tsarin shari’a da shari’ar Musulunci.
Hukumar ta ce ta tilasta shigar da kara a kan ma’auratan ne bayan kokarin da Majalisar Shawarar Musulunci (Shura) da Masarautar Tsafe suka yi tun a shekarar 2020 bai haifar da da mai ido ba.
Lauyan hukumar Malam Sani Muhammed ya shaidawa kotun cewa binciken da hukumomin addinin musulunci daban-daban da masarautar suka gudanar ya nuna cewa ma’auratan da suka yi aure tun wani lokaci a shekarar 1999 suna da alaka kai tsaye don haka an haramta aure a tsakaninsu.
Muhammed ya ce matakin ya sabawa koyarwar Addinin Musulunci kamar yadda aka yi nuni a cikin Alkur’ani sura ta uku aya ta 23.
Don haka ya roki kotu da ta gaggauta raba auren.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa Tsafe, yana da ‘ya’ya takwas tare da matarsa.
(NAN)