Wata babbar Kotu da ke zamanta a Gusau, babban birnin jihar Zamfara ta rushe shugabancin jam’iyyar APC a dukkan matakan jihar.
Wani Alhaji Surajo Garba da wasu mutum 138 abokan siyasar Sanata Kabir Garba Marafa ne suka shigar da ƙarar neman kotun ta soke zaben shugabannin.
Masu ƙarar sun kafa hujjar cewa ba a bi kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba wajen gudanar da zaɓen na shekarar 2018 da ya kawo shugabancin waɗanda ake ƙarar.
Sun kuma ce ba a basu dama sun shiga zaɓen ba, don haka suka nemi kotun da ta ayyana shugabannin jami’yyar tun daga matakin mazaɓu har zuwa na jiha a matsayin haramtattu.
https://dimokuradiyya.com.ng/covid19-likitoci-8-sun-kamu-da-cutar-covid19-a-jihar-zamfara/
Da yake yanke hukuncin, Mai Sharia Bello Tukur Gummi ya ce ya gamsu da hujjojin da masu shigar da ƙarar suka shiga kuma an yi zaɓen shugabanin jami’yyar bisa ƙa’ida ba.
Alkalin ya kuma hana waɗanda kotun ta sauke daga gabatar da kawunansu a matsayin shugabanni jam’iyyar.
Ya kuma umarci a yi sabon zaɓen shugabannin jamiyar a kuma tabbatar an yi wa kowan adalci ta hanyar bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
To sai dai lauyan shugabannin jam’iyyar APC da hukuncin ya shafa a jihar, Barista Kelechi Odeoyegbo ya ce suna duba yiwuwar ɗaukaka ƙara.