Hausawa dai na cewa ko babu ciwo idan ajali yayi kira dole a tafi, ita kuwa wannan Amarya ana tsaka da bikinta, nata ajalin ya riske ta.
Amaryar mai suna Immaculate Okochu ta gamu da ajalinta ne bayan da ta hau babur na acaba a lokacin da take kan hanyarta na zuwa wajen aiki, inda wata tirela ta yi kanta ta kuma take ta a yankin Ajah a Legas.
An garzaya da Immaculate asibiti domin ceto rayuwarta, amma kafin a samu nasarar ceto rai yayi halinsa.
Kawar marigayiyar, Lucy Ibe, wacce ita ke jagorantar tsare-tsaren bikin amaryar da ake shirin yi, ta shaida wa BBC cewa amaryar ta rasu ne a ranar Laraba 12 ga watan Agusta, ranar da babbar motar ta take ta.
https://dimokuradiyya.com.ng/mutane-5-sun-rasa-rayukansu-a-wani-hatsarin-mota-a-jihar-anambra/
“Ba nan take ta mutu ba, da fari an kai ta wani asibiti a yankin da lamarin ya auku, daga nan kuma aka kai ta babban Asibitin gwamnati da ke Marina a cikin garin Legas.
“A lokacin da na je asibitin na iske ta a bayan motar da aka kai ta asibitin ana ba ta agajin gaggawa, an sanya mata ruwa, ba a kai ga karbar ta a cikin asibitin ba ta mutu.
‘Yan uwa da abokan arzikin amaryar sun yi ta sanya hotonta a kafafen sada zumunta domin nuna alhini da kuma mika ta’aziyya.