Wata uwa ‘yar shekara 23 mai suna Mary Olatayo ta sayar da jaririnta dan kimanin sati uku da haihuwa a kan kudi naira 600,000, kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta bayyana.
‘Yan sanda sun cafke Olatayo ne a ranar 18 ga watan Agusta, biyo bayan korafin da mahaifin jaririn ya yi a hedikwatar ‘yan sandan Mowe dake jihar Ogun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: NAAT Ta Dakatar Da Yajin Aikin Watanni 3
Mahaifin jaririyar ya shaida wa ‘yan sanda cewa yana da alaka da ita, wanda hakan ya kai ga daukar ciki da samun jaririn da ake magana a kai.
Mutumin ya bayyana cewa lokacin da Mary ta samu juna biyu, ya samar mata da hayar wani gida wanda take zaune har ta haifi da namiji.
A cewarsa, kwatsam Olatayo ta bace da jaririn daga gidan haya bayan makonni uku da haihuwa.
An ce ta koma wani otal, inda ta tafi don yin ‘ƙugiya’ da wani mutum.
“Duk kokarin da aka yi na sanin inda jaririn ya kasance ya ci tura,” kakakin ‘yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ruwaito mutumin yana fadin hakan.
Oyeyemi ya sanar da cewa DPO na sashen Mowe, SP Folake Afeniforo, da ke aiki da rahoton, ya yi cikakken bayani kan jami’an da suka gudanar da bincike a wurin, kuma an kama wanda ake zargin.
Yayin da ake yi mata tambayoyi, Oyeyemi ya ce Olatayo “ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta sayar da jaririn ga wani a jihar Anambra a kan kudi Naira dubu dari shida.”
“Ta kuma yi ikirarin cewa kawarta, Chioma Esther Ogbonna ce ta kai ta wajen mai saye a jihar kuma duk sun raba kudin daidai gwargwado.”
Majiyar Jaridar DIMOKURADIYYA ta samu cewa ikirarin Mary Olatayo ya kai ga kama Chioma, wanda Oyeyemi ya ce ya kuma tabbatar da ikirarin Mary.
Binciken ‘yan sanda, Oyeyemi ya nuna cewa, Olatayo ‘yar asalin Omu-Aran a jihar Kwara “wata yarinya ce da take ganin jaririn a matsayin ya dagula kasuwancinta, don haka ta yanke shawarar cefanar da jaririn.”
Ya kara da cewa Olatayo tana da wata abokiyar ta Chioma, haifaffiyar jihar Imo, “wanda ta tuntubi mai siyan da sauri a jihar Anambra.”
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wadanda ake zargin zuwa sashin yaki da fataucin bil’adama da aikin yara na CIID na jihar domin ci gaba da bincike.
CP Bankole ya kuma ba da umarnin cewa dole ne a yi duk abin da doka ta tanada don kwato jaririn da aka sayar.
A wani labarin kuma 2023: Atiku Ya Saba Shan Ƙasa, Tinubu ne Zai Lashe Zabe – Gwamna
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya bayyana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin gogaggen wanda ya saba faduwa zaɓe.
Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya sha neman kujerar shugaban kasa amma yana shan kaye.