By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun cafke wata ‘yar aikin gida mai suna Favor Iwuozor ‘yar shekara 14 bisa zargin sace dan uwargidanta mai shekaru biyu da haihuwa.
Kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi, shine wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Abeokuta ranar Talata.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin a unguwar Sagamu da ke jihar bayan da wata mai suna Victoria Nwafor ta shigar da kara a sashin ‘yan sanda na Sagamu.
Ya bayyana cewa Nwafor ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta ga wata yarinya ‘yar shekara 14 a ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2021, tare da wani yaro dan shekara biyu mara lafiya a Yaba dake jihar Legas.
“Ta kara da cewa yarinyar tana rokon sadaka ne bisa zargin cewa karamin yaron kaninta ne kuma iyayensu sun mutu a wani hatsarin mota a watan Disambar shekarar 2020.
“Saboda tausayawa matar ta tafi da su duka zuwa gidanta da ke Sagamu domin kula da tabarbarewar lafiyar yaron.
“Amma nan take yaron ya samu sauki sosai, wanda ake zargin ya so ya kai yaron jihar Imo shi kadai kuma hakan ya sa matar ta yi zargin cewa akwai matsala bara ta kai kara ga ofishin ‘yan sanda.
“Bayan rahoton, ofishin ‘yan sanda DPO Sagamu, CSP Okiki Agunbiade, ya yi cikakken bayani kan masu binciken da za su kawo yarinyar domin yi musu tambayoyi.
“Da aka yi mata tambayoyi, yarinyar ta amsa cewa ita baiwa ce ga mahaifiyar yaron kuma ta tafi da yaron ne a ranar 19 ga watan Disamba, 2021, da nufin kai shi Amraku Umorsu a karamar hukumar Isiala/Mberna dake jihar Imo.
“Ta kara da cewa ta dauki jaririn ne daga cocin a lokacin makarantar Lahadi, kuma tun da malamin makarantar ya san ta tare da mahaifiyar jaririn,saboda haka ba ta da matsala da malamin don haka ya sake mata yaron.
“Ta kuma yi bayanin cewa ta yanke shawarar yin bara ne domin ta kara samun kudin sufuri zuwa jihar Imo,” in ji PPRO.
Sannan ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a tuntubi iyayen jaririn, yayin da aka mika karar zuwa rundunar jihar Legas inda aka aikata laifin.