Wata Daga cikin Alhazawan Jahar Taraba ta Ɓace a Saudiyya
Ɗaya daga cikin alhazai 668 da suka fito daga jihar Taraba zuwa aikin hajjin da aka kammala a kasar Saudiyya, an sanar da ɓacewar ta.
An bayyana cewa mahajjaciyar da ta Ɓace mai suna Hassan Abdullahi Bamuze ta Ɓace daga cikin rukunin alhazai biyu da suka isa jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mata Suna Buƙatar Samun Kuɗi Kafin Su Shiga Siyasa — Inji Mai Sharhi
Da yake tabbatar da rahoton ranar Asabar a Jalingo, Babban Birnin Jihar, Jami’in Hulɗa da Jama’a (PRO) na Hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar, Baba Hamza Muri, ya ce har yanzu ba a gano mahajjaciyar mace da ta Ɓace ba.
Hukumar ta ce an samar da hanyoyin da suka dace don gano ta kuma ta gano cewa “Hukumar Hajji ta Najeriya ta bada tabbacin cewa za su yi duk mai yiwuwa don taimaka mana mu gano ta.”
Ya ce jihar ta kammala aikin Hajjin shekarar 2022 cikin nasara tare da isar da kaso na karshe na maniyyata 131 daga kasar Saudiyya a yau.
“Alhazan jihar sun fara komawa gida ne bayan kammala aikin Hajji tare da alhazai 536 a ranar Asabar da ta gabata, hukumar ta yi farin ciki da cewa aikin ya samu nasara.”
Wasu daga cikin mahajjatan da suka zanta da wakilinmu sun bayyana atisayen a matsayin mafi kyawu da Hukumar ta taba gudanarwa a jihar.