Wata gobara ta kone wasu gidaje da shaguna kulle da kadarori na miliyoyin Naira a kusa da titin Mile 50 a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a titin Aliubala Eze.
Mataimakin Sufeton ‘yan sandan jihar, Mista Yakubu Zekeri, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels, ya ce ba a rasa rai ba.
Ya kuma bayyana cewa babu daya daga cikin mutanen da ke cikin ginin da ya samu raunuka.
A cewar Mista Zekeri, shiga tsakani da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka yi a kan lokaci ya taimaka wajen hana tashin gobarar zuwa wasu gine-gine da ke kusa da inda gobarar ta tashi.