By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani yaro mai suna Sulaiman Usaini dan shekara daya da mahaifiyarsa mai suna Zainab Yusha’u mai shekaru 25 a duniya a hanyar Gwarzo daura da Gidan Kaji a Kano.
Alhaji Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano.
Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar.
“Mun sami kiran waya da misalin karfe 07:00 na safe. daga wani Usman Nura kuma nan take na aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 07:08 na safe,” inji shi.
Abdullahi ya ce gini ne wanda ba beni ba yana da tsayi kusan mita 35 da 20 ft da ake amfani da shi a matsayin mazaunin, daki daya ya kone yayin da gobarar ta kone falon gaba daya.
Ya ce an mika gawarwakin wadanda abin ya shafa ga mijin matar Zainab, Malam Usaini.
“Da kyakkyawan kokari na jami’an kashe gobara, mun sami damar shawo kan gobarar domin kada ta bazu zuwa gidan makwabta,” in ji shi.
Sai dai kakakin ya shawarci jama’a da su bi ka’idojin tsaro domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.