Daraktan hukumar samar da irin noma ta kasa wato NASC a takaice, Dr Philip Ojo ya ce Nijeriya ta fara dawo wa turba mai kyau tun bayan da ta rufe kan iyakar kasarta tare da takaita zuba kudade a asusun FOREX wato na kasar waje domin ganin an rika shigo da kayayyakin abinci musamman ma shinkfa.
Ojo, wanda Dr Ishiak Khalid, ya wakilce shi a yayin wani taro da NASC din ta shirya a Abuja shi ne ya bayyana hakan. Taron an yi masa take da; ‘Samar da ingantaccen iri cikin sauki da arha ga manoman Nijeriya.”
Ojo ya tabbatar da cewa; rufe kan iyakokin Nijeriyar zai taimaka wajen magance matsalar samar da abinci da matsalar tsaro a kasarnan.