Jami’ar kimiyya ta Akure, FUTA da ke kudu maso yammacin kasarnan ta dakatar da wasu dalibai da suka yi wa wata daliba taron dangi suka yi mata dukan tsiya ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.
An yi ta ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan da wani bidiyo ya bayyana wasu dalibai na yi wa wata daliba wacce ta ke ajin farko dukan fitar hankali.
Kakakin makarantar Adegbenro Adebanjo ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a wajen makarantar.
Adebanjo ya ce “A halin da ake ciki, mun dakatar da dalibai bakwai da ke da hannu a lamarin. Mun dakatar da karatunsu kuma bayan mun kammala bincike za su san makomarsu. Ba za mu amince da cin zarafi ba, babu wanda zai tsallake fushin hukuma a cikinsu.”
FUTA ta ki bayyana sunan daliban har sai sun gama bincikensu.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Akure, Femi Joseph ya ce wani ya kira shi don kai kara kan lamarin kuma ya ba shi shawarar zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Rundunar ta ce idan lamarin ya faru ne a cikin makaranta dole ne ta bi ta hukumar makaranta kafin ta iya kama wani mai laoifi amma idan a wajen makaranta lamarin ya faru, to za su iya kama duk wani mai laifi kai tsaye.
A halin yanzu, hukumar makarantar ta sallami dalibar da aka yi wa duka daga asibiti kuma ana ba ta shawarwari.