A daren jiya ne fitacciyar Jarumar Finan-finan Hausa ta Kannywood wacce ta yi shura a kwanakin baya kuma har yanzu zarenta ke ja wato Nafisat Abdullahi, ta wallahi hoton ta su uku da Jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi wanda aka fi sani da Mahmud cikin shiri mai dogon zango na Labarina da kuma Maryam Waziri da ake kira Laila duk cikin shirin na Labarina, a shafin Instagram.
Da ma dai Laila cikin shirin Allah Ya tarfa wa garin ta nono kasantuwar daula da Allah Ya jefa ta a ciki, lamarin da ya kai ga ta saye soyayyar Nafisa da Nuhu Abdullahi wacce tun farko sun gina ta ne bisa tafarkin gaskiya ba wai don kudi ba.
Ga masu bibiyar shirin na Labarina sun ga yadda duniya ta juyawa Nafisat baya tare da yi mata tsayuwar gwamen Jaki, wanda ya kai ga har an yi yunkurin aure tsakanin Laila da Mahmud.
To sai dai daga bisani al’amarin ya ci tura domin Laila ta hau kujerar naki ta kame kam cewa atafau sai ta san asalin Mahmud gabannin ci gaba da soyayyar tasu.
Ko da ya dake daga bisani Maryam Waziri wacce aka fi saninta da Laila a shirin sun yi mummunar rabuwa da Mahmud sakamakon abinda ta kira da rashin sanin asalin nasa, to amma hakan bai hana Nafisat Abdullahi nuna kishin ta ba Inda har ya kai ga ta wallafa a shafin Instagram din nata mai suna Nafisat Abdullahi Official cewa yau za a yi ta ta kare, kuma ta yi hakan cikin fushi amma da raha kamar yadda jaruman fina-finai suka saba.
Sakon ta “Yau za’ayita ta kare, ko ni Laila*🙅❤️💋💞
Yanzu haka a halin da ake ciki Nafisat Abdullahi tuni ta koma gurin tsohuwar zuma wato tsohon saurayinta Lukman wanda da ma dan gidan masu shi ne da kuma ya yi karatu a kasar waje.
Abinda dai jama’a ma’abota shirin ke tsumayar gani shine yadda za ta kaya tsakanin Mahmud da Laila da ita Nafisat Abdullahi da ake kira Sumayya cikin Labarina.