Wakilinmu Musa Ahamed Gumel
Babbar Kotun jihar Jigawa mai lamba ta 8 dake garin Gumel ta daure Garba Ismail Birnin Kudu da kuma Auwalu Jibril shekaru 12 kowannensu a gidan Yari bisa lefin sama da fadi da kudade har naira miliyan 250.
Alkalin kotun mai shari’a Ado Yusif Birnin Kudu yace hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ce ta gabatar da mutanen biyu a gaban kotun bisa zargin karbar na goro har naira miliyan 250 daga cikin kudi naira Biliyan dubu 23 da miliyan 290 da aka rabawa jihohin kasar nan 36 domin yin magudin babban zaben kasar nan na 2015
Garba Ismaila ma’aikaci ne a kwalejin ilmi ta jihar Jigawa dake Gumel da kuma Auwal Jibril mataimakin Darakta a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Dutse, sun karbi kudin ne daga hannun tsohuwar ministar man fetir Mrs Diezeni Madueke, ta hannun bankin Fidelity domin rabawa manyan ‘yan siyasa da nufin aikata magudin zaben.
Mai shari’a Ado Yusif yace bayan kotun ta ji ta bakin shedu, ta kama mutanen biyu da aikata lefuka guda uku da suka hadar da aikata rashin gaskiya a matsayinsu na ma’aikata da karbar kudade ba tare da izinin hukuma ba da kuma karba da bada cin hanci da rashawa wanda hakan ya sabawa sashe na tara karamin sashe na daya na dokar cin hanci da rashawa ta 2000 da sashe na 122 na penal code na dokar jihar Jigawa ta 2012
Kotun ta kuma bada umarnin kwace dukkannin kadarorin Garba Ismail da suka hadar da naira miliyan 17 dake asusun ajiya na bankin GT da Unity da gidaje tara da filaye 8 dake jihohin Kano da Jigawa da manyan motoci guda uku da kuma kudi naira miliyan 11 mallakar Auwal Jibril dake bankin Jaiz.