Wata kotu ta yankewa wani dalibi mai shekaru 20 mai suna Usama Abubakar, kan tuhumar sa da satar jakar sawa Aljihu, (wallet) ta wani mai hayar mashin yayin da abokin sa ya dau mai mashin din.
Abubakar, dai ya amsa laifukan da ake tuhumar shi da su inda ya nemi afuwar su da cewa ba zai Kara ba.
Mai Shari’a a kotun Majistire, Hauwa Yusuf, ta ce ta yanke hukuncin ne domin ya yi dai dai da sashi na 157 a dokar laifuka.
Kuma ta Bashi damar ko ya biya kudin Tara ta dubu goma, daya laifin kuma tace ko yayi zaman wakafi na wata biyar cin amana ko tarar dubu biyar 5000, mai gabatar da kara sajan bala Muhammad, ne ya tabbatar da kama mai laifin da kuma yadda suka damke shi.