By Abbas Yakubu Yaura
Kotun Majistare ta daya da ke Gusau babban birnin jihar ta yanke hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso ga wani lauyan karya da aka kama a jihar Zamfara, Chukwuka Jude.
Alkalin kotun, Sa’adu Gurbin-Bore, ya ce bayan da ya amince da aikata laifin, an yanke wa wanda ake kara hukunci.
“Yin zamba da magudi laifuka ne da za a iya hukunta su a karkashin sashe na 179 da na 324 na kundin tsarin mulki da hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku da zaman gidan yari na shekara bakwai tare da tara ko duka biyun,” in ji shi.
Sai dai lauyan wanda ake kara, Joseph Eze, ya bukaci alkalin kotun da ya yi adalci da jin kai, kasancewar wanda ake tuhumar dan gida ne mai yara bakwai marasa aikin yi.
Ya kara da cewa “Wanda ake tuhumar ya kuma samu barkewar gobara sau biyu, don haka akwai bukatar a yanke masa hukunci mai sauki.”
Amma babban alkalin kotun ya ce, “Bisa la’akari da rokon da lauyan wanda ake kara ya yi, Chukwuka Jude an yanke masa hukuncin daurin shekara daya a gidan yari saboda samunsa da laifin yin magudi.
“An kuma yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ko kuma biyan tarar naira 50,000 a matsayin wani zabin aikata laifin.”
Ya ce idan ba a biya tarar ba, wanda aka yanke wa hukuncin zai yi zaman gidan yari biyu a lokaci guda.