Wata kotu dake Legas ta yankewa wani mutum zaman gidan kaso har abada
Wata babbar kotu a Legas dake yankin Tafawa Balewa a ranar Talata ta yankewa wani ma’aikacin karfi Philp Ikechi Alias mai shekaru 32 hukuncin zaman gidan kaso har abada bayan ya kashe abokinsa.
KARANTA:-Yan bindiga sunyi garkuwa da wani Hakimi da Iyalansa
Mai shari’a Modipe Nicol-Clay ya yanke hukuncin kan wani tsohon laifi da yakai shekara shida saboda wasu matsaloli irin su Covid-19 da kuma yajin aikin maaikatan wurin.
Ade shekar 2014 Yan sanda suka kama Ikechi inda suka damka shi a wata kotun majistret .
An Mai da shari’ar zuwa wata babbar kotu dake Legas inda gwamnatin Legas ta dauki nauyi yin bincike akan wanda ake tuhuma akan kisa.
Masu karar suke gayawa kotu lamarin ya auku ne a ranar 14 ga watan Aprilu shekarar 2014 misalin karfe 8:30 a Plank Bridge dake garin Kemberi a Okokomaiko a Jihar Legas.
Daga karshe dai kotu ta tabbatar da Ikechi tare da abokansa sun kashe Puadbe Yaige ta hanyar soka masa wuka.
Sai Ikechi bai tabbatar da laifin sa ba sannan aka fara musayar dalilai.
A lokacin da yake kokarin Kare kansa yake cewa shi baya ko kusa da inda lamarin ya auku lokacin kisan Yaige.
Sai mai shari’ar ta tabbatar da mai kara ya gabatar da hujjoji gamsassu Wanda suke tabbatar da wanda ake kara yayi karya.
Tace domin tabbatar da karyar da yayi ta gabatar da mutane biyar wadanda shaidune suka bayyana yadda kisan Yaige ya wakana.
Daga karshe dai Alkalin ya tabbatar da wanda ake kara Yana da laifi Kuma Yananan lokacin da lamarin ya auku.
Comments 1