Wata kotun shari’ar Musulunci ta Kano ta raba auren Asiya Abdullahi Ganduje ‘yar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, mai shekaru 16 da aure.
Asiya ta garzaya kotu tana neman a raba aurenta da mijinta, Inuwa Uba, saboda ta gaji da zaman aurensa wanda suka haifi ‘ya’ya hudu.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Alkalin kotun, Khadi Halliru Aliyu ya raba auren ne a lokacin da yake yanke hukunci kan lamarin a ranar Alhamis.
KU KARANTA KUMA Wata Kotu Ta Datse Igiyar Auren Wata Uku Da Daurawa
Sai dai Khadi Aliyu ya umarci diyar Ganduje da ta mayar wa mijinta Uba, sadakinsa Naira 50,000 a matsayin asarar da ya yi.
Kotun ta kuma yi watsi da bukatar mijin Asiya na neman takardun kadarorin da ya ce nasa ne.
Lauyan wanda ya shigar da kara ( diyar Ganduje), Ibrahim Nassarawa, ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bisa abin da ya kamata ya zama tushen auren wanda shi ne sadaki.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Da yake mayar da martani kan hukuncin, Lauyan maigidan Umar I. Umar ya ce za su yi nazari kan hukuncin kuma za su jira mataki na gaba daga wanda yake karewa kan ko za su kai ga kotun daukaka kara a kan lamarin ko a’a.
Ya ce sun yi iya kokarinsu wajen daidaita dangantakar da ke tsakaninsu musamman yadda ta haifa masa ‘ya’ya hudu amma ba a samu sakamakon da ake so ba.
A Wani Labarin Kuma An Ceto Mutane Hudu Yayin Da Wani Gini Ya Ruguzo A Rukunin Gidajen Gwarinpa
An ceto mutane hudu daga baraguzan ginin da ya ruguje a ranar Alhamis a rukunin gidajen dake Gwarinpa, a Abuja.
Mista Kenneth Chigelu, Shugaban hulda da jama’a na hukumar kula da gidaje ta tarayya (FHA) ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.