Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta amincewa gwamnatin jihar Kano ta ciyo bashin Naira biliyan 10 Don amfani da su wajen sanya na’urar CCTV.
A baya dai kotun ta dakatar da gwamnatin bayan da wata kungiyar mai zaman kanta Wato Kano First Forum ta shigar da karar neman dakatar da gwamnatin Kanon.
A wannan lokacin kotun ta amince da dakatar da gwamnan, zuwa lokacin da zata gama saurara karar, kuma yayin zaman kotun na ta janye dakatarwar baya, inda yanzu ta amincewa Gwamna Abdullahi Ganduje don Ciyo bashin.
Mai shari’a AM Liman na babbar kotun tarayya da ke kan titin Gyadi Gyadi Kano a yau Talata ya yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da kara Yusuf Isiyaku Rabiu ya yaudari kotu a shari’ar, don haka an cire dokar ta wucin gadi a shari’ar.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Liman ya ci gaba da cewa a cikin hukuncin da ya yanke, wanda ya shigar da karar ya yi kuskure wajen shigar da karar saboda haka umarnin ya rasa wurin da za a ci gaba da shi kuma a soke shi.
Alkalin kotun ya mika karar zuwa ga alkali mai zaman kansa a Abuja yayin da kotun ta tafi hutu domin ci gaba da bayar da umarnin shiga tsakani a gaban kotun kan wannan karar.
Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar Kano ta nemi amincewar majalisar dokokin jihar ta karbo bashin Naira biliyan 10 domin aikin na CCTV.
Tuni dai aka ruwaito cewa majalisar dokokin jihar ta amince da wannan lamuni.