Kotun tarayya dake zaman ta a Abuja ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta INEC daga dakatar da yin rijistar katin zabe ga yan kasa.
A baya dai hukumar ta sanar da cewa zata dakatar da yin rijistar ga daukacin Najeriya, nan da zuwa karshen watan Yunin 2022.
Alkalin kotun mai Shari’a Mobolaji Olajuwon a yau Litinin, ya tabbatar da cewa hukumar zabe ta dakata daga kudirin hana ci gaba da yin rijistar.
Hukunci ya biyo bayan sauraron ɓangaren masu kara, wanda suka shigar da karar kalubalantar hukumar kan kin kara wa’adin rijistar zaben.
Kungiyar SERAP mai fafutukar tabbatar da adalci ce ta shigar da karar gaban kotu, tana mai kafa hujja da cewa hukumar a baya ta kara wa’adin zaben fidda gwanin dan takarar.
Yanzu haka dai tuni mai Shari’a Mobolaji Olajuwon ya dage ci gaba da sauraron shari’ar, zuwa nan da ranar 29 ga watan nan da muke ciki.
Baya ga SERAP akwai karin wasu yan kasa na gari da suka hada gwiwa da kungiyar wajen shigar da karar, don neman kotu ta sanya hukumar ta kara wa’adin yin rijistar.