Kungiyar yaki da cin zarafin kananan yara da cin zarafin jinsi (AACSGB) ta yi kira da a dauki matakin gaggawa don kawar da duk wani nau’in cin zarafin yara a kasar nan.
Misis Ufuoma Akpobi, Kodinetar kungiyar ta AACSGB, reshen Edo, ta yi wannan kiran a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Benin a ranar Alhamis.
Akpobi ta ce cin zarafin yara gaskiya ce da yake aukuwa a duk fadin duniya baki daya a kuma cikin dukkan al’ummomi da al’adu.
Ta ce hakan yana haifar da illa ga walwalar yara da amfanin su a cikin gidajen su da al’ummomin su.
”Laifukan cin zarafin yara musamman, jima’i da su da kuma fataucin mutane na ƙaruwa.
”Muna da buƙatar aiwatar da dokoki masu ƙarfi domin hukunta masu cin zarafin yara domin su zama misali ga ‘yan baya”
”Ya kamata shugabannin gargajiya da na alumma su shiga cikin wayar da kan jama’a kan illolin cin zarafi ga yara.
“Yawan wadanda dangi ke cin zarafin yara masu kananan shekaru yana da ban tsoro; mafi yawan lokuta wadanda abin ya shafa ba sa samun adalci saboda dangin na rufa musu asiri, ”in ji ta.
Hadin gwiwar kungiyar AACSGB sun ba da shawarar a samar da tsauraran dokoki kan masu laifi don rage yawan cin zarafin yara da yin jima’i da su
“Ya kamata a karfafa rukunin masu ba da shawara da sanya su cikin makarantu domin koyarwa da ba da shawara ga yara kan rahoton cin zarafin mata,” in ji ta.