By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyoyin farar hula a karkashin kungiyar masu fafutukar tabbatar da gaskiya da rikon amana, sun yi kira da a kafa kotun yaki da rashawa ta musamman. Kungiyoyin CSO sun bayyana cewa irin wannan kotun za ta gaggauta gudanar da shari’ar laifukan cin hanci da rashawa.
Shugaban gudanarwar kungiyar TAN na kasa, Olukunle Adeogun, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron manema labarai domin bayyana ayyukan da aka shirya domin bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya a shekarar 2021.
Adeogun yace kotun ta musamman zata kuma taimaka wajen rage nauyin kararraki da dama.
Sannan yace cin hanci da rashawa babban laifi ne da zai iya gurgunta ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a dukkanin al’ummomi kuma babu wata kasa ko yanki ko al’umma data kare.
Kazalika ya yi kira ga gwamnatoci dasu samar da matakan da zasu sa mutane ko kungiyoyi su yi wahala wajen sace dukiyar al’umma.Ya ce, “Kotu ta musamman za ta taimaka wajen saukakawa alkalan kasar dake fama da shari’a da dama kuma hakan yana shafar tsarin shari’a.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “kungiyar tace suna kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa data Jiha dasu samar da dokokin kafa wannan kotu.sannan duk da haka, muna kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su dauki matakan kariya don yaki da cin hanci da rashawa maimakon matakan yaki da su.”