Wata kungiya karkashin inuwar jam’iyyar APC a jihar Delta mai suna Delta APC Unity Forum ta bukaci ƴaƴan jam’iyar da su guji kama karya wanda wasu shugabannin jam’iyyar ke kokarin yi.
Kungiyar ta ce shugabannin jam’iyyar na kokarin ɗoki ɗora a babban taron jam’iyyar da zai gudana nan gaba kadan.
Kungiyar ta ce wannan kira ya zama wajibi lura da irin yadda shugabannin ke kokarin sanya masu uwa a gindin murhu cikin wannan tsari, inda ta ce kuma suna haka ne don cimma wata manufa a shekara ta 2023.
Ko-odinetan kungiyar Olusegun Isaac Ewhere wanda shine ya bada wannan shawara, ya ce daga cikin masu wannan yunkuri akwai Sanata mai ci a jihar, wanda ake ganin yiwuwar tsayawr shi takarar gwamnan a shekara 2023.
Ewhere ya kara da cewa ɓaraka da ta kunno kai a jam’iyyar a baya ta taimaka matuka wajen wargajewar ta, iuma har yanzu wadanda suka kitsa ta a baya ba su daddara ba.