By Abbas Yakubu Yaura
Wata kungiya a karkashin kungiyar Arewa Support Group for Igbo President, ta yi kira ga jam’iyun APC da PDP da su marawa yankin Kudu maso Gabas baya a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
Ko-odinetan kungiyar na kasa Mustapha Imam ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a Kano a yammacin ranar Alhamis.
Ya ce kiran ya zama wajibi domin inganta hadin kan kasa da tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a kasar.
Imam ya ce, “Mun hada hannu da kungiyoyin masu ruwa da tsaki, ra’ayoyi, wajen neman matsayar wanda za mu mara wa baya a babban zaben 2023 mai zuwa.
“A karshen shawarwarin da muka yi, mun cimma matsayar ne domin tabbatar da daidaito, adalci, hadin kai da kuma ci gaban tarayyar Najeriya na tallafa wa yankin Kudu maso Gabas don samar da shugaban kasa mai zuwa.”
Ya kara da cewa tun daga shekarar 1999 zuwa yau aka fara wannan tsarin dimokuradiyya, dukkan shiyyoyin sun samar da shugaban kasa sai Kudu maso Gabas.
Sannan Imam ya ce kungiyar za ta ci gaba da hada kan sauran ’yan uwa da kungiyoyin da ke fadin kasar nan don neman taimako da goyon bayan yankin Kudu maso Gabas don samar da shugaban kasa a 2023.
Ya ce kungiyar a shirye take ta goyi bayan duk wani dan takara mai gaskiya kuma kwararre daga yankin ba tare da la’akari da siyasarsa ba.
“Kungiyar Arewa Support Group for Igbo President a shirye take ta goyi bayan duk wani mai sahihanci kuma ƙwararren ɗan takara wanda zai iya bayar da gudummawa ba tare da la’akari da siyasar sa ba,” in ji shi.