Kwalejin fasaha ta Abubakar Tatari Ali dake jihar Bauchi ta dakatar Raliya Kashim daga bakin aikin ta.
Kwalejin ta zargi malamar da shiga harkokin siyasa duk da kasancewar ta Malama a kwalejin.
Mai magana da yawun kwalejin Malam Maikano Baraya ne ya tabbatar da hakan cikin wata Sanarwa da aka fitar ga manema labarai, a yau Juma’a a jihar Bauchin.
Baraya ya kara da cewa Raliya tana amfani da shafin ta na Whatsapp wajen tallata wasu yan takara da suka haɗar da dan takarar shugaban kasa da kuma gwamna.
Ya ce ”malamar ta wallafa wani sako dake dauke da tallan yan siyasa, maimakon abinda zai karar da al’umma domin ci gaban su.
Hakan ya sanya kwalejin daukar matakin dakatar da ita, domin bata damar ci gaba da harkokin siyasar ta, tun da wannan layin ta dauka, kuma take ganin zai bulle mata,” inji Baraya.