Wata Mata da ta yi tsalle ta fada kogin Lagoon a legas a ranar Alhamis da yamma an bayyana sunan ta da Adetutu Adedokun, an gano ma’aikaciyar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
Majiyar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, wasu majiyoyi a ofishin sun bayyana cewa ita mai koyar da yaki ce da ba ta da makami wacce ta shiga alfarmar iyayenta da ke aikin kayan tufafi.
Kamar yadda gidan Talabijin na Channels ta ruwaito, ‘yan watannin da suka gabata, Adedokun wacce ta cika shekara 30 da haihuwa, ta samu wasikar yabo daga babban daraktan hukumar ta DSS a matsayin wacce ta fi kowa yaki a tawagarta.
An kuma bayar da rahoton cewa saurayin wadda lamarin ya shafa ya nemi aurenta makonnin da suka gabata. Ta sauka daga motar haya ta Uber a kan gada kuma ta fada cikin lagon ranar Alhamis da yamma. Direban tasi ya yi ikirarin cewa tana zazzafan kalamai da angonta kafin ta sauka daga motar.
Jim kadan bayan faruwar lamarin, sai ga jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas, LRT, da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas (LASWA), da jami’an hukumar DSS, suka dauki matakin nemo wadda abin ya shafa.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, Babban Sakataren na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, LASEMA, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’ar nan, ya kuma ce har yanzu tawagar masu aikin ceto na nan kan ruwan suna kokarin gano gawar.
A Wani Labarin Kuma Fadar Shugaban Kasa: Najeriya Zata Kasance Cikin Aminci Karkashin Mulkin Tinubu – Aisha Buhari
Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, ta bai wa ‘yan Najeriya tabbacin shugabancin jam’iyyar APC, mai rike da tutarta Bola Tinubu.
Aisha Buhari ta ba da tabbacin cewa Najeriya za ta zauna lafiya a karkashin jagorancin Tinubu.