By Abbas Yakubu Yaura
Wata mata da ‘ya’yanta uku sun tsallake rijiya da baya a garin Ilorin na jihar Kwara a ranar Talata bayan da wata kwantena da ake sarrafa ta, ta fado a kan motarsu dake shatale-talen Garage Offa.
Kwantenan, a cewar shaidun gani da ido, ta fado ne daga kan wata tirelar dakon kayan nauyi bayan da direban ya yi kokarin zagayawa cikin sauri, alokacin ta fada kan motar bas din da suke ciki.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa matar da ‘ya’yanta uku sun makale a cikin motar bas sama da sa’o’i uku, kafin daga bisani hadin gwiwar jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kwara, da hukumar kiyaye hadurra ta tarayya da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya suka ceto su.
Wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, tace an ceto mutanen hudun da ransu sannan aka kai su asibintin koyarwa na Jami’ar Ilorin.
Adekunle yace, “Matar da take tuka bas din da ‘ya’yanta uku, namiji da mata biyu, an ceto su da ransu daga motar. Sun samu raunuka kuma an kai su asibiti.