A safiyar yau Asabar da misalin karfe takwas na safe Yan sanda suka yi dirar mikiya a gida mai lamba 16 a kan layin Donking, a cikin Nsugbe dake karamar hukumar Anambara Ist, don chafke wata mata wacce aka kama dumu dumu ta chakawa Mijinta Wuka a kirji.
Don tabbatar da zargin an tuntubi mai magana da yawun bakin yan sandan Jihar Anambara, Harunna Muhammed, ya kuma tabbatar da haka inda yace, Caji ofis din Yansanda na (33) dake Onitsha, sun damke matar mai suna Makoduchukwu Ndubisi.
Matar mai shekaru 20, ta kashe mijinta ne bayan sun sami wata hatsaniya ta fusata ta chaka mishi wuka jini face face.
Faruwar hakan aka garzaya da shi babban Asibitin , Boromeo, dake Onitsha don ceto rayuwar sa daga baya likita ya tabbatar da mutuwar sa.
Yan sanda sun tabbatar da tsunduna binciken gaggawa game da batun.