- Wata mata ta kashe wata jaririya a unguwar Works Layout, Owerri.
- Ta ce Yesu ne ya umarce ta daga sama ta kashe yarinyar.
- Tuni ‘yan sanda suka kama ta, za kuma su kaita kotu da zarar an kammala bincike.
Wata mata da har yanzu ba a bayyana wacece ba ta daɓawa wata yarinya wuƙa har lahira a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
An ce wacce ake zargin ta shiga wani gida ne ta kuma daɓawa jaririyar gidan wuƙa.
Lamarin ya faru ne a ranar 28 ga watan Mayu a Works Layout, Owerri, babban birnin jihar, PREMIUM TIMES ta rawaito.
Wani faifan bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda mazauna garin suka fusata suna yi wa wacce ake tuhuma da kisan tambayoyi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Haifi Wani Jariri Da Yatsu Takwas A Ƙasar Chana
“Wacece wannan yarinyar da kika dauki da wuƙa kika kashe ta, ƙaramar yarinya ce fa?” wata murya ta dakawa matar tsawa cikin turancin pidgin.
A cikin faifan bidiyan, an ga yarinyar da aka kashe mai kimanin shekaru biyar da haihuwa, wata mata da ake kyautata zaton mahaifiyarta ce ta ɗakko ta daga cikin harabar gidan.
Mahaifiyar wanda aka kashe, cikin kuka, da alama tana ƙoƙarin kai yarinyar asibiti.
Mazaunan da suka fusata sun gangaro kan wanda ake zargin, wata budurwa ‘yar shekara 20 da haihuwa – suka yi mata duka tare da jan ta da ƙarfi.
Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ta aikata wannan aika-aika, matar ta ce Yesu ne ya aiko ta ta kashe yarinyar.
“Yesu ne da sama ya aiko ni ya ce in kashe ta,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa “Ku kai ni ofishin ‘yan sanda, Idan na isa wurin (‘yan sanda), to su harbe ni, su yi duk abin da suka ga dama da ni.”
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye a ranar Juma’a, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES faruwar lamarin, amma bai bayyana sunan wanda ake zargin ba.
Mista Okoye, mataimakin sufeton ‘yan sanda, ya ce an kama budurwar, inda ya ce za ta fuskanci shari’a bayan kammala bincike bincike.