Wata mata mai shekaru 30 a duniya Hadiza Ayuba, ta haifi ‘ya mace a filin kwallo dake karamar Hukumar Dawakin Kudu, daidai lokacin da take kan layin karbarar kayan haihuwa da na jarirai kyauta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa taron bayar da tallafin an shirya shine ga mata masu juna biyu, a yankin karamar hukumar Dawakin Kudu, wanda dan majalisar tarayya na karamar hukumar hadin gwiwa da asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
A wannan karo, an shirya tallafawa mata 900 daga mazabu 30 na kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa, kamar yadda ma’ajin jam’Iyar APC na mazabar Dawaki Babannan Bala ya shaidawa manema labarai.
KARANTA ANAN: Rikicin PDP: Ayu Zai Sauka, Tsagin Wike Za Su Fitar Da Shugaban Jam’iyya
Lamarin dai ya faru ne yau Asabar, daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da taron, bayan jami’an lafiya daga Asibitin Malam din suyka kammala yiwa matan masu juna bita.
Da faruwar lamarin ne kuma sai aka garzaya da ita bayan kangon filin taron domin bata kulawa ta musamman, an kuma bata nata tallafin kai tsaye wanda ya kunshi tallafin ya kunshi bahon wanka da sauran kayayyakin da mai jego ke bukata.
A wani labarin kuma: Da Dumi-Duminsa: Sheikh Aisami: Rundunar Soja Ta Kori Jami’anta Guda Biyu
Rundunar sojin Najeriya ta kori wasu sojoji biyu da ke aiki da bataliya ta 241 da ke Nguru a jihar Yobe bayan samunsu da laifuka guda biyu.
A cewar Mukaddashin Kwamandan Bataliyar, Laftanal Kanal Ibrahim Abdullahi Osabo, an samu wadanda ake zargin da laifuka biyu; wato: rashin yin aikin soja; da kuma nuna son zuciya ga horon yin hidima, kamar yadda DAILYPOST ta bayyana
Wadanda ake zargin dai an rage musu mukamansu daga ma’aikatan kofur zuwa na sirri kafin sallamar su gaba daya.