Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta kama Maryam Habibu, ‘yar shekara 18 da haihuwa, bisa zarginta da nutsar da Dan Kishiyarta mai shekaru hudu a cikin rijiya da ke karamar hukumar Kafur ta jihar. Kamar yadda Daily Post ta ruwiato.
Maryam wadda ta fito daga kauyen Leko da ke karamar hukumar Danja tare da wasu mutane 11 da ake tuhuma da laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami da satar shanu, an baje kolin su ne a ranar Juma’a a hedikwatar ‘yan sanda da ke Katsina.
KARANTA WANNAN LABARIN: Oyetola Ya Dage Cewa Shi Ne Lashe Zaben Gwamnan Osun
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, yayin da yake zantawa da manema labarai yayin baje kolin masu laifin, ya bayyana cewa an kama matar ne a ranar 9 ga Nuwamban shekarar 2022.
Ya ci gaba da bayyana cewar ta fita da yaron ne kuma ta jefa shi cikin rijiya.
A cewar Kakakin rundunar, Maryam da mahaifin yaron sun rabu da juna
Maryam wadda ta zanta da manema labarai cikin harshen Hausa, ta amince da aikata laifin, inda ta ce, lamarin kaddara ne
A cewarta, “Gaskiya ne na jefa yaron a cikin rijiyar da ya mutu amma, daman Allah ya kaddara cewa zai mutu a ranar. Shi ya sa ya rasu.”
A wani labarin kuma, Tinubu Da Jiga-Jigan APC Sun Isa Jihar Delta
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da wasu jiga-jigan jam’iyya mai mulki sun je Delta ranar Asabar domin yakin neman zaben 2023.
Da yake jawabi a lokacin kaddamar da yakin neman zaben, Tinubu ya ba da tabbacin cewa shugabancinsa da kuma gwamnan Omo-Agege zai kawo “Kwarin Gwauiwa, aiki, ci gaba ga Delta da Najeriya baki daya.”