Rundunar tsaron jama’a ta Nijeriya: Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), a jihar Borno ta kama wata mata; yar shekaru 38, Hauwa Adamu, wadda ake zargi da kona yar kishiyarta, yar shekara bakwai a duniya, inda ta hanyar dadara mata dutsen guga cike da wuta ga al’aurarta.
Kwamandan rundunar NSCDC a jihar Borno, Mista Abdullahi Ibrahim, shi ne ya sanar da hakan, a lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN), a ranar Laraba, a birnin Maiduguri.
Haka kuma, kwamandan ya bayyana cewa rundunar su ta samu rahoton abkuwar lamarin ta hanyar wani bawan Allah wanda ya tausaya wa halin da karamar yarinyar ta shiga.
Sannan kuma ya shaidar da cewa Malam Hauwa ta aikata wannan danyen aiki ga karamar yarinyar, wai saboda ba ta jin magana. Sannan kuma binciken farko da su ka gudanar ya gano yadda wadda a ke zargin ta sha azabtar da karamar yarinyar kala-kala. Mista Ibrahim ya ce yarinyar ta fada wannan yanayin ne ta dalilin rabuwar mahaifan ta. Bugu da kari kuma ya ce sun mika lamarin yarinyar zuwa hukumar yaki da safarar jama’a ta kasa domin cigaba da gudanar da bincike da daukar matakin da ya dace.