By Abbas Yakubu Yaura
Wata mata mai suna Eziada Chika Mbachu, ta kubuta daga hannun danta, wanda ya daba mata wuka a wurare da dama domin ya yi amfani da mahaifiyar tasa wajen yin tsafi .
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin, tsakanin karfe 7 na safe zuwa karfe 8 na safe a gidan Heroes kusa da otal din Concord dake Owerri.
A cewar wani ganau da ya zanta da jaridar Vanguard ya ce matashin ne ya gayyaci mahaifiyar tasa da sanyin safiyar Litinin inda ya farmaki mahaifiyar tasa da wuka a wurare dama.
Game da yadda matar ta tsere, ya ce: “Mahaifiyar tana ihu tana kira da a taimaka mata da tabon jini da raunuka a jikinta. Makwafta suka ji haka, sai suka yi gaggawar taimaka mata. Suka cece ta. Da dan ya ga mutane da yawa suna zuwa sai ya daina kai wa mahaifiyar tasa hari.
“A lokacin ne mahaifiyar ta fadi ta fara kuka sai makwabta suka ceto tare da raba ta da dan.
“Kamar yadda nake magana da ku, an garzaya da matar zuwa cibiyar kula da lafiya ta asibitin tarayya domin a yi mata magani nan take saboda yankan wukar dake jikinta. ‘Yan sanda sun kama yaron tare da kai shi ofishin su.”
A cewar ta “Na gode wa Allah da ya cece ni. Na gode wa Allah da ya kubutar da ni. Ina gode wa makwabtana da suka cece ni. Ina godiya ga duk wanda ya kawo min dauki. Ina godiya ga makwabta.”
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, PPRO, Micheal Abbattam, ya ce ba a yi masa bayani ba, kuma ya yi alkawarin kiran DPO na yankin da lamarin ya faru.”
Comments 1