By Abbas Yakubu Yaura
Wata matar aure ‘yar shekara 30 mai suna Fulera Lawal, a ranar Larabar data gabata ta roki wata kotun shari’a dake Magajin Gari Kaduna da ta umarci mijinta, Kabir Abdulhamid ya biya ta alawu-alawus din abinci na shekara biyu.
Fulera wanda ke zaune a unguwar Doka da ke Kaduna, ta shaida wa kotu cewa Abdulhamid ya watsar da ita a gidan iyayenta tun daga shekarar 2020 kuma iyayenta sun rika ciyar da ita da dansu.
Fulera ta kuma roki kotu da ta umurci Abdulhamid da ya dauki nauyin yaron nasa daga yanzu.
Alkalin kotun, Murtala Nasir, ya umurci Fulera da ta lissafta adadin kudaden da take nema a matsayin alawus alawus na ciyarwa na tsawon shekaru biyu sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Janairu.