Wata Mata a Kasar Ghana ta gamu da ajalin ta a yayin da take gudun wuce kima don zuwa tabbatar da labarin da aka bata na cewa mijin ta yana tare da wata a waje suna aikata alfasha.
Wata ce dai da ba a bayyana sunan ta ba ta kai gulmar wa matar inda ta ce mata a lokacin suna tare, ita kuwa ba tare da wata-wata ba ta zari mota sai hanya.
Kuma gabannin isar ta gurin da aka tsegun ta mata ne dai ta gamu da hatsari inda nan take ta ce ga garin ku.
Kawo yanzu dai hukumomi a kasar ba su ce uffan ba dangane da wannan bakon al’amari.
To sai dai kamar yadda aka sani harkokin yan farka a tsakanin mazan wannan zamani musamman a nahiyar Afirka na ci gaba da ta’azzara, duk da cewa an ce idan bera na da sata to daddawa ma nabda wari.