By Abbas Yakubu Yaura
Wata matashiya mai shekaru 33 mai suna Lucy Jacob, wacce ake zargin ta siyar da wani yadin leshi da kudin sa ya kai Naira 65,000 a ranar Alhamis ta gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Kaduna.
Wanda ake tuhumar wanda take zaune a Sabon Tasha, Kaduna, ana tuhumarta da laifin rashin gaskiya da kuma zamba.
DUBA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattawa Ta Amince Da Mambobin Kwamitin Kula Da Harkokin Kudi 7 Na CBN
Sai dai kuma wadda ake tuhumar ta musanta zargin aikata laifin.
Lauyan masu shigar da kara, Insp Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa mai shigar da kara, Ms Sarah Victor, ta dauki kayan yadin leshi da kudin sa ya kai Naira 65,000 zuwa shagon wanda ake kara a watan Disambar shekarar 2021, amma wadda ake kara ta sayar da kayan.
Lauyan mai gabatar da kara ya yi zargin cewa wanda ake kara, wanda ta yi alkawarin mayar da kudaden a cikin kashi-kashi, ta yi watsi da alkawarin data dauka.
Leo ya shaidawa kotun cewa a yayin binciken ‘yan sanda, wanda ake zargin ya amsa laifin sayar da kayan ga wani abokin ciniki.
A cewar mai gabatar da kara, laifin ya sabawa tanadin sashe na 339 da 321 na kundin laifuffuka na jihar Kaduna na shekarar 2017.
Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Emmanuel ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira 100,000 tare da wasu mutane biyu da za su tsaya mata, wadanda dole ne su nuna shaidar biyan haraji.
Sannan ya dage cigaba da sauraron karar har sai zuwa ranar 24 ga watan Mayu domin sauraren karar.
(NAN)