- Wata mata ta nuna yadda rana ke da zafi a Dubai, masarautar Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin da take amfani da shi wajen soya kwai.
- A cikin wani faifan bidiyo da @mercy_gains1 ta saka, matar ta sanya kaskon suya a ƙarƙashin rana, ta zuba mai a ciki.
- Mutane sun cika da mamaki lokacin da ta fasa kwai a cikin kaskon, nan take ya fara soya kamar yana cin wuta.
Wata mata da ke zaune a Dubai a UAE ta ba mutane mamaki ta hanyar amfani da rana wajen toya kwai.
Matar ta ce ta samu wannan nasarar ne ba tare da amfani da iskar gas ko wani makamashin girki ba saboda a fili rana ta na da zafi sosai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cikon da ta yi a mazaunanta sun faɗo lokacin da take tsaka da taka rawa.
A cikin wani faifan bidiyo da @mercy_gains1 ta wallafa , matar ta fito da kaskon soya ta ajiye a karkashin rana mai zafi.
Matar tana soya ƙwai a ƙarƙashin rana, kwalbar mai ta kawo ta zuba a kaskon soya. Sai ta fasa kwai biyu a cikin kaskon, sai ya fara soyuwa.
Da farko dai matar ba ta saka takalmi ba, amma ga dukkan alamu zafin ranar dake yasa sai da ta saka takalmi.
Lamarin dai ya ba wa mutane da dama mamaki, inda wasu ke cewa tabbas kaskon ya yi zafi kafin a fito da shi waje.
Wasu mutane sun shiga shakkar ta, suna masu cewa ba zai yiwu a soya ƙwai da hasken rana kaɗai ba.
Martani daga masu amfani da TikTok @Joanna ta ce: “Wane ne yake tunanin kaskon daga wuta ne.”
@ sharhi: “A nan Saudiyya, rana tana iya dafa wake.”
@Habib Beye ya mayar da martani: “Amma kuma ki cire takalmanki.”
@ user2001509101289 ya ce: “Ina gaya muku. “Ni ma ina kuka lokacin da zan je aiki saboda zafin rana,”
@loverboy ya ce: “Waɗanda ke Dubai ne kaɗai za su iya fuskantar hakan.”
@E & V ya yi sharhi: “Tuni an gama saka kaskon ya yi zafi sosai. Kin ce rana, amma meyasa baki saka takalmi ba lol.”