Batun yiwuwar sauyin shekar kaftin din Barcelona Lionel Messi zuwa PSG na cigaba da yin karfi a ‘yan makwannin nan, bayan da fitacciyar mujallar wasanni ta France Football ta wallafa kanun wani sharhi dake cewa ‘Wasikar kungiyar PSG ta sirri’ tare da wallafa hoton gwarzon dan wasan sanyen da rigar kungiyar ta Paris Saint Germain.
Sai dai za a iya cewa a nata bangaren PSG na yin taka tsantsan wajen fitowa fili kan aniyar kula yarjejeniya da Messi, har sai koma ya tabbata.
A watan Disambar bara tauraron PSG Neymar ya sha alwashin ya zama dole a wannan karon ya koma taka leda tare da Messi, yayin da a watan Janairu, daraktan wasannin PSG Leonardo ya ce kulla yarjejeniya da manyan ‘yan wasa irinsu Messi shi ne burinsu.
A dai watan na Janairu ne kuma, dan wasan tsakiya na kungiyar ta PSG Leandro Paredes yace tuni suka soma tuntubar kaftin din na Barcelona don haka a yanzu wuka da nama na hannunsa.